4 Mayu 2020 - 03:41
​Ivory Cost: Firayi Minista Ya Nufi Faransa Domin Duba Lafiyarsa

Firayi ministan kasar Ivory Coast ya nufi birnin Paris na kasar Faransa domin duba lafiyarsa.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran AFP daga birnin Abijan ya bayar da rahoton cewa, ofishin firayi ministan kasar Ivory Coast ya sanar da cewa, a daren jiya Firayi ministan kasar Amadou Gon Coulibaly ya nufi birnin Paris na kasar Faransa domin duba lafiyarsa.

Bayanin ya ce Coulibaly ya isa birnin Paris, kuma tuni aka fara duba lafiyarsa, kuma a halin yanzu karamin ministan tsaro na kasar Hamid Bakayeko shi ne ke gudanar da ayyukansa na wucin gadi, sai dai bayanin bai yi ishara da matsalar da ke damun Coulibaly ba.

A karshen watan da ya gabata ne Amadou Gon Coulibaly ya killace kansa, bayan da ya gana da wani jami'i wanda daga bisani ta bayyana cewa yana dauke da cutar corona, amma daga bisani Coulibaly ya fito ya ci gaba da harkokinsa, a ranar Juma'a ma da ta gabata ma ya halarci bikin ranar ma'aikata da aka gudanar a kasar.

Amadou Gon Coulibaly dan shekaru 61 da haihuwa, shi ne dan takarar jam'iyya mai mulki a zaben shugaban kasa da za a gudanar a kasar Ivory Coast a cikin watan Oktoba mai zuwa, bayan da shugaban kasar mai ci a yanzu Alassane Ouattara ya sanar da cewa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar ba.



/129